Main Article Content
Ra'in Zahiranci a Cikin Waƙar Baka: Tsokaci a Kan Waƙar Mai Akwai da Babu ta Alh. (Dr) Adamu Ɗanmaraya Jos O Sentido da Existência na Poesia Oral: Uma Reflexão sobre a Poesia do Presente e do Não-Presente por Alh. (Dr.) Adamu Danmaraya Jos
Abstract
Wannan bincike mai taken Ra'in Zahiranci a Cikin Waƙar Baka: Tsokaci a Kan Waƙar Mai Akwai da Babu ta Alh. (Dr) Adamu Ɗanmaraya Jos, ya yi dubin irin gudummawar da mawaƙan baka na Hausa suke bayarwa ta fannin wa'azantarwa da hannunka mai sanda ga al'umma musamman masu kuɗi. Wannan dubi kuwa an yi shi ne ta ɓangaren tarbiyya, domin gyara kayanka bai zamo sauke mu raba ba. Kamar yadda yake cikin waƙar mai akwai da babu. Makasudin wannan aikin shi ne bayyanar da irin gudummawar da waƙa musamman ta baka take bayarwa ga al'umma ta fannin gyaran hali. An yi amfani da wallafaffun littattafai masu dangantaka da aikin sai kuma aka nazarci ita waƙar, a matsayin hanyoyin bincike. Sannan binciken ya kawo bayanin ra'in zahiranci da manufofinsa kamar yadda Mustapha (2013) da Gambo (2017), suka kawo a cikin ayyukansu, domin a wannan ra'in ne aka ɗora aikin. A cikin binciken an kawo misalan yadda mai akwai yake kallon maras shi, sannan aka yi ɗan jan hankali ga shi mai akwai domin ya gane dukiyarsa ba ta sanya Allah ya fifita shi a kan talaka ba, wadda daga ƙarshe ko mutuwa ya yi launi da adadin yadin da za a nannaɗe shi da wadda za a naɗe talakan da shi duk iri ɗaya ne, sannan dukkansu biyun a rami za a binne su bayan mutuwarsu.
Esta pesquisa, intitulada Ra'in Zahiranci a Cikin Waqar Baka: Tsokaci a Kan Waqar Mai Akkaiwa da Babu, do Dr. Adamu Danmaraya Jos, examinou a contribuição dos poetas orais hauçás no campo da pregação e do ensino à comunidade, especialmente aos ricos. Este estudo foi realizado sob a perspectiva da educação, pois consertar seus pertences não é algo que possamos compartilhar. Como no poema Mai Akkaiwa da Babu, o objetivo deste trabalho é revelar a contribuição que a poesia, especialmente a poesia oral, traz à comunidade no campo da reforma moral. Livros publicados relacionados à obra foram utilizados e o próprio poema foi analisado como métodos de pesquisa. O estudo, então, explicou o conceito de Zahiranci e seus objetivos, conforme Mustapha (2013) e Gambo (2017) trouxeram em suas obras, pois é nesse conceito que o trabalho se baseou. No estudo, foram dados exemplos de como os ricos olhavam para os pobres, e então foi dada uma pequena atenção ao rico para que ele percebesse que sua riqueza não fazia com que Deus o preferisse aos pobres, que no final, ou na morte, a cor e a quantidade de tecido a ser enrolado e aquele a ser enrolado no pobre são todos iguais, e ambos serão enterrados em um buraco após a morte.



